Lafiya Jari Ce
Yadda ake samun ƙaruwar mace-macen kwab-ɗaya ko kuma mutuwar fuju’a
- Autor: Vários
- Narrador: Vários
- Editora: Podcast
- Duração: 0:10:13
- Mais informações
Informações:
Sinopse
Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon ya nazarci yawaitar mace-macen kwab-ɗaya ko kuma mutuwar fuju’a da ake ganin ta’azzararsu a wannan lokaci musamman a sassan Najeriya a wani yanayi da matsi ko kuma tsadar rayuwa ke ci gaba da galabaitar da jama’a. Dai dai lokacin da masana ke alaƙanta wannan matsala ta mutuwar far ɗaya da wasu kwantattun cutuka da yanayi kan tayar da su a lokaci guda, wani bincike baya-bayan nan ya danganta tsananin damuwa da yawaitar tunane-tunne halin rayuwa a matsayin ummul aba’isin kamuwa da wasu cutuka da ke kisan jama’a. Tuni dai masana a ɓangaren kiwon lafiya suka tsananta kiraye-kirayen ganin jama’a sun mayar da hankalin wajen sanin halin da lafiyarsu ke ciki don kaucewa mutuwar ta kwaf ɗaya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.......