Tambaya Da Amsa

Informações:

Sinopse

Masu Saurare na aiko da Tambayoyinsu domin neman amsa a shirin, Ana gabatar da shirin ne a karshen mako.

Episódios

 • Tambaya da Amsa - Dalilan da suka haddasa tawaye a Chadi (2)

  Tambaya da Amsa - Dalilan da suka haddasa tawaye a Chadi (2)

  15/05/2021 Duração: 20min

  A cikin shirin 'Tambaya Da Amsa' Michael Kuduson ya kawo amssoshin tambayoyin da wasu daga cikin masu sauraronmu suka aiko mana, ciki har da amsa a kan tambayar da ke neman musabbabin rikicin tawayen Chadi da sauransu. A yi sauraro lafiya.

 • Tambaya da Amsa - Dalilan da suka haddasa tawaye a kasar Chadi

  Tambaya da Amsa - Dalilan da suka haddasa tawaye a kasar Chadi

  08/05/2021 Duração: 20min

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon tare da Michael Kuduson ya tattauna kan batutuwa da dama da suka hada da waiwaye kan yadda tawaye ya samo asali a kasar Chadi.

 • Tambaya da Amsa - Amsa: Mene ne Cookis da kuma ci gaban hira da mawakiya Aishatou Dankwali

  Tambaya da Amsa - Amsa: Mene ne Cookis da kuma ci gaban hira da mawakiya Aishatou Dankwali

  01/05/2021 Duração: 20min

  Shirin 'Tambaya Da Amsa' kamar kowane mako, tare da Michel Kuduson yana zakulo wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraro suka aiko mana ne, ya karanto su, kana ya samar da amsoshinsu ta wajen gudummawar kwararru. A wannan mako, shirin ya taho da tambayoyi da amsoshi, daga cikinsu akwai wacce karin bayani kan Cookis na Intanet da kuma ci gaban hira da daya daga cikin mayakiyar tawagar Sogha a jamhuriyar Nijar Aishatu dankwali. 

 • Tambaya da Amsa - Hukuncin dake hawa kan wadanda suka ki biyan bashin Bankin Duniya ko IMF

  Tambaya da Amsa - Hukuncin dake hawa kan wadanda suka ki biyan bashin Bankin Duniya ko IMF

  03/04/2021 Duração: 19min

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon kamar yadda aka saba ya nemi karin bayani kan jerin tambayoyin da masu sauraro suka aiko masa, ciki har da fashin baki kan ka'idojin karbar bashi daga hukumomin kasa da kasa da suka hada da Bankin Duniya ko IMF, sai kuma hukuncin dake hawa kan wadanda suka ki biyan bashin da suka karba.

 • Tambaya da Amsa - Tambaya :Saudiyya ta zake a kan yakin Yemen?

  Tambaya da Amsa - Tambaya :Saudiyya ta zake a kan yakin Yemen?

  27/03/2021 Duração: 19min

  Menene ya sa saudiyya ta zake a kan yakin Yemen, kuma me ya sa yanzu ta mika tayin tsagaita wuta tsakaninta da ‘yan tawayen Houthi na kasar? Alama ce ta wannan yaki na daf da karewa? Bala, a game da wannan tambaya taka, wakilinmu na Kaduna a Najeriya Aminu Sani Sado ya gana da Malam Ibrahim Gwandu, malami a kwalejin kimiyya da Fasaha ta Kaduna, wato Kaduna Polytechnic, kuma mai sharhi a kan al’amuran siyasar duniya a cikin shirin Tambaya da amsa daga RFI tareda Michael Kuduson.

 • Tambaya da Amsa - Tambaya Da Amsa: Maanar dokar-ta-baci

  Tambaya da Amsa - Tambaya Da Amsa: Ma'anar dokar-ta-baci

  20/03/2021 Duração: 19min

  A cikin shirin 'Tambaya Da Amsa' na wannan mako, Michael Kuduson ya karanto tambayoyin masu sauraro, kana ya kawo amsoshinsu tare da taimakon kwararru. Daga cikin tambayoyin da aka amsa, har da wadda ke neman sanin ma'anar dokar-ta-baci. A yi sauraro lafiya.

 • Tambaya da Amsa - Banbanci tsakanin kasashen da ake kira Jamhuriya da kuma Tarayya

  Tambaya da Amsa - Banbanci tsakanin kasashen da ake kira Jamhuriya da kuma Tarayya

  06/03/2021 Duração: 20min

  A cikin shirin 'Tambaya Da Amsa' Michael Kuduson ya kawo amsar wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko, ciki har da amsar tambayar da ke neman banbaci tsakani kasashen da ake kira Jamhuriya, Tarayya da kuma Jamhuriyar Demakradiya

 • Tambaya da Amsa - Wai shin da gaske babu gwamnati a kasar Somalia ?

  Tambaya da Amsa - Wai shin da gaske babu gwamnati a kasar Somalia ?

  27/02/2021 Duração: 19min

  Shirin 'Tambaya Da Amsa' na wannan mako tare da Michael Kuduson ya kawo amsar wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko, ciki har da amsar tambayar da ke neman wai ko da gaske ne babu gwamnati a kasar Somali da kuma me ne ne alfanun kungiyar kasuwanci ta duniya WTO.

 • Tambaya da Amsa - Amsa kan dalilan da suka sa aka gaza samun galaba a kan Bashar al -Assad na Syria

  Tambaya da Amsa - Amsa kan dalilan da suka sa aka gaza samun galaba a kan Bashar al -Assad na Syria

  20/02/2021 Duração: 19min

  A cikin shirin 'Tambaya Da Amsa' Michael Kuduson ya kawo amsar wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko, ciki har da amsar tambayar da ke neman dalilan da suka sa duk da taron dangi aka gaza hambarar da gwamnatin shugaban Syria, Bashar Al Assad.

 • Tambaya da Amsa - Karin bayani kan sabon nauin cutar Korona

  Tambaya da Amsa - Karin bayani kan sabon nau'in cutar Korona

  06/02/2021 Duração: 20min

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon kamar yadda ya saba, ya tattauna da masana kan wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraro suka aiko, ciki har da neman karin bayani kan sabon nau'in cutar coronavirus.

 • Tambaya da Amsa - Ya aka yi Bahause ya yi wa mai suna Abubakar Inkiya da Garba?

  Tambaya da Amsa - Ya aka yi Bahause ya yi wa mai suna 'Abubakar' Inkiya da 'Garba'?

  30/01/2021 Duração: 19min

  Shirin 'Tambaya Da Amsa tare da Michael Kuduson ya amsa wasu daga cikin tambayoyin masu sauraro ne. Daga cikin tambayoyin da ya kawo amsoshinsu , akwai wacce ke neman sanin yadda Bahaushe ya samo inkiyar 'Garba' da ya ke wa 'Abubakar', da kum yadda 'yan kasasehnwaje da ke zaune a Najeriya za su yi a game da umurnin gwamnatin kasar na hada layin waya da lambar dan kasa.

 • Tambaya da Amsa - Bayani a kan Youtube

  Tambaya da Amsa - Bayani a kan Youtube

  12/12/2020 Duração: 19min

  A cikin shirin 'Tambaya Da Amsa' na wannan mako, Michael Kuduson ya karanto, tare da lalubo amsar tambayoyin da wasu daga cikin  masu saurarnmu suka aiko mana, ciki har da amsar tambaya a kan yadda dandalin Youtube yake, da yadda ake samun kudi a cikinsa.

 • Tambaya da Amsa - Yadda ake gane kasa ta shiga matsin tattalin arziki

  Tambaya da Amsa - Yadda ake gane kasa ta shiga matsin tattalin arziki

  05/12/2020 Duração: 19min

  A cikin shirin 'Tambaya Da Amsa'  Michael Kuduson ya karanto tambayoyin masu sauraro, yayin da kwararru suka samar da amsoshinsu.

 • Tambaya da Amsa - Musababin rikicin yankin Tigrea a Habasha

  Tambaya da Amsa - Musababin rikicin yankin Tigrea a Habasha

  28/11/2020 Duração: 19min

  Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya gana da manzanin kungiyar kasashen Afrika ta AU a Addis Ababa, a wani hukunrin su na samar da mafita a yakin da ake tsakanin dakarun Habasha da na yankin Tigrea. A cikin shirin Tambaya da amsa,Michael Kuduson ya amsa wasu daga cikin tambayoyin masu saurare dangane da rikicin Tigrea.

 • Tambaya da Amsa - Tarihin yadda kasar Israila ta kafu da dalilan da suka sa ta yi karfi

  Tambaya da Amsa - Tarihin yadda kasar Isra'ila ta kafu da dalilan da suka sa ta yi karfi

  14/11/2020 Duração: 20min

  Shirin 'Tambaya da Amsa' na wannan makon ya yi karin bayani kan tarihin kafuwar kasar Isra'ila da kuma yadda ka yi tayi karfi wajen sarrafa manyan gwamnatocin kasashen duniya. Shirin ya kuma cika alkawarin karin bayani kan tsarin sake fasalin gudanar gwamnati a Najeriya da wasu masu ruwa datsaki ke cigaba da yin kiraye-kirayen aiwatarwa.

 • Tambaya da Amsa - Bayani a kan tsamin dangantaka tsakanin Amurka da Iran

  Tambaya da Amsa - Bayani a kan tsamin dangantaka tsakanin Amurka da Iran

  07/11/2020 Duração: 19min

  A cikin shirin 'Tambaya Da Amsa na wannan mako, Michael Kuduson ya karanto tambayoyin da wasu daga cikin masu sauraronmu suka iko mana, tare da samar da amsoshinsu da taimakon kwararru. Ayi sauraro lafiya.

 • Tambaya da Amsa - Bayyanin sake fasalin kasa, wato restructuring

  Tambaya da Amsa - Bayyanin sake fasalin kasa, wato restructuring

  31/10/2020 Duração: 19min

  Masu sauraren sashen hausa na rediyon Farnasa Rfi sun nemi bayani a game da sake fasalin kasa, wato restructuring da wasu ke ta neman a yi a Najeriya. Michael Kuduson ya ji ta bakin masana a cikin shirin tambaya da amsa.

 • Tambaya da Amsa - Alakar rance da kuma karya darajar Naira a Najeriya

  Tambaya da Amsa - Alakar rance da kuma karya darajar Naira a Najeriya

  03/10/2020 Duração: 19min

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon tare da Michael Kuduson ya tattauna kan batutuwa da dama da suka hada da batun karbar rancen kudi da kuma karya darajar Naira a Najeriya kafin ta samu damar cin bashi daga kasashen duniya.

 • Tambaya da Amsa - Amfanin katin Air Doctor ga lafiyar jikin dan adam

  Tambaya da Amsa - Amfanin katin 'Air Doctor' ga lafiyar jikin dan adam

  26/09/2020 Duração: 19min

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon kamar yadda aka saba ya nemi karin bayani kan jerin tambayoyin da masu sauraro suka aiko masa, ciki har da  neman sanin alfanun katin da wasu manyan mutane suka fara likawa a kirji kamar ID card, da ake ce wa ‘Air Doctor’.

 • Tambaya da Amsa - Ko yan Najeriya na biyan haraji ?

  Tambaya da Amsa - Ko yan Najeriya na biyan haraji ?

  12/09/2020 Duração: 19min

  A makon da ya gabata ,Michael Kuduson ya jiyo ta bakin masana dangane da tambayar masu saurare  da suka bukaci amsa dangane da wannan tambaya ,ko yan Najeriya na biyan haraji? A cikin wannan shirin  ga dai amsar masana a kai.

Página 1 de 2