Sinopse
Shirin yakan diba kasuwancida tattalin arizikin kasashen duniya ya ke ciki. Shirin yakan ji sabbin dubaru da hajojin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masanaantu dangane da halin da suke ciki.
Episódios
-
Yadda matasa suka rungumi kananan sana’o’i lokacin azumin Ramadana a Damagaram
03/04/2024 Duração: 09minShirin Kasuwa a Kai Miki Dole a wannan makon ya maida hankali ne kan kananan sana’o’i da matasa ke yi don samun na abinci a lokacin azumin watan Ramadana a Damagaram da ke jamhuriyar Nijar. wasu daga cikin sana'oin da matasan sukafi mai da hankali akai dai sun hada da bredi ko kayan marmari ko kayan lambu da dai sauransu. Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Ahmed Abba.......
-
Gidauniyar Dangote ta kashe naira biliyan 15 na tallafin abinci a Najeriya
27/03/2024 Duração: 10minShirin Kasuwa A Kai Miki Dole a wannan makon ya maida hankali ne kan rabon tallafin abincin naira biliyan 15, da Gidauniyar Aliko Dangote ta kaddamar a Najeriya. Wannan dai na daga cikin matakan rage radadin talauci a tsakanin al'ummar Najeriya, da gidauniyyar hamshakin attajirin Afirka ta kaddamar a birnin Kano da ke arewacin kasar. Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Ahmed Abba.......
-
Yadda matsin rayuwa ya tilastawa 'yan Najeriya fasa rumbunan abinci
06/03/2024 Duração: 10minShirin Kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan makon ya yada zango ne a Tarayyar Najeriya, inda ya yi dubi kan matsanancin kuncin rayuwar da al’umman kasar suka shiga da har ta kai ana fasa rumbunan abinci ko tare manyan motocin dakon kaya a tituna ana kwasan abinci.
-
Yadda al'ummar kasashen yammacin Afrika ke kokawa saboda tsadar rayuwa
28/02/2024 Duração: 09minA wannan makon shirin Kasuwa akai miki dole, zai yi duba ne game da bakar ukubar da al’ummar kasashen Nahiyar Africa ke fuskanta, a sanadiyar hauhawar farashin kayayyakin masarufi, musamman kasashen Nijeriya, Nijar da kuma Cameroon. Yanzu haka dai a iya cewa wannan yanayi na hauhawar farashin kayan masarufi tuni ya zame wa kasashen Nijeriya da Nijar da Ghana da kuma Cameroon Dan zani a kasuwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Abdulkadir Haladu Kiyawa.....