Sinopse
Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu
Episódios
-
Ra'ayoyin masu saurare kan gudummawar marigayi Issa Hayatou ga kwallon ƙafa
12/08/2024 Duração: 10minA makon jiya ne Allah ya yiwa tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Afirka Issa Hayatou rasuwa, bayan gajeruwar rashin lafiya. Hayatou da ya kwashe kusan shekaru 30 yana jagorancin hukumar, ya taka rawa sosai wajen ci gaban kwallon kafa a nahiyar, musamman bangaren matasa da kuma ganin an kara wa kasashen Afirka gurbi a gasar cin kofin duniya daga gurabe 2 zuwa 5.Shin kun gamsu da gudumawar da ya bayar?Kamar da me za ku tuna wannan gwarzo?
-
Ra'ayoyin ƴan Najeriya kan jawabin shugaba Tinubu game da zanga-zanga
05/08/2024 Duração: 09minShugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci al’ummar ƙasar su jingine zanga-zanga tare da bayyana aniyar tattaunawa don laluɓo masalaha. A jawabin da ya gabatar sakamakon zanga-zangar tsadar rayuwa da ta ɓarke a akasarin sassan ƙasar, Tinubu ya shaida wa ƴan Najeriya cewa yana jin raɗaɗin da suke ji, kuma tabbas zai samo mafita.Yaya wannan jawabi nasa ya riske ku?Ko ya taɓo batutuwan da suke ci wa al’umma tuwo a ƙwarya?Wace shawara za ku ba wa masu zanga-zanga?
-
Ra'ayoyin masu saurare kan shigar iyayen al'umma cikin ayyukan garkuwa da mutane
30/07/2024 Duração: 10minShirin ra'ayoyin ku masu saurare na wannan rana ya duba yadda rashin tsrao da kuma garkuwa da mutane ke kara yawaita a arewacin Najeriya, inda a baya-bayan nan kwamishin yan sandan jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ya sanar da cafke 'dan majalisar dokoki da hakimi tare da tsohon shugaban karamar hukumar Kaurar Namoda bisa zarginsu da hannu dumu dumu cikin ayyukan garkuwa da mutane domin karbar kuɗin fansa. Wannan al’amari ya sake tabbatar da zargin da ake yi wa wasu daga cikin shugabanni a Najeriya dangane da taka muhimmiyar rawa a matsalolin tsaron da suka addabi al’ummar ƙasar.Me za ku ce kan wannan lamari?Wane darasi ya kamata al’umma su koya?Wace mafita ce mafi dacewa a bi wajen magance matsalolin tsaron dake tagayyara jama’a?Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin, tare da Nasiruddeen Muhammad
-
Ra'ayoyin masu saurare kan karuwar hare-hare a kasashen Sahel da kewaye
29/07/2024 Duração: 09minShirin ra'ayoyin masu saurare na wannan rana ya mayar da hankali ne kan yadda kungiyoyin mayaka masu ikirarin jihadi ke kara zafafa hare-hare a kasashen yankin Sahel. Hare-haren mayakan ya fara tsallakawa zuwa kasashen Jamhuriyar Benin da Togo wadanda basu saba ganin irin haka a kasashen su ba.Ina ne kuke ganin ya kamata mahukunta su kara azama don samun zaman lafiya mai dorewa?Wace gudunmowa zaku bayar a matsayinku na al'umma don tabbatuwar tsaro a kasashen ku?Wannan shine maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a yau.