Sinopse
Muna gabatar muku da shirye-shirye masu ayatarwa da suka shafi al´adu da zamantakewa tsakanin al´ummomi da mabiya addinai daban-daban da nufin kyautata tsarin zamantakewa da fahimtar juna ta hanyar tuntuar juna da shawarwari tsakani ba tare da nuna fifiko akan wani ba.
Episódios
-
Taba Ka Lashe: 15.12.2021
21/12/2021 Duração: 09minAn gudanar da bikin nadin sababbin sarautu, a masarautar Hausawan Turai. Karin bayani cikin Taba Ka Lashe.
-
Taba Ka Lashe: 08.11.2021
14/12/2021 Duração: 09minMata na taka muhimmiyar rawa, wajen magance rikice-rikicen kabilanci da na addinai da makamantansu. Shirin Taba Ka Lashe.
-
Taba Ka Lashe: 24.11.2021
30/11/2021 Duração: 09minKo kun san yadda mabiya darikun Sufaye ke ziyara Kushewar Waliyai a Maroko? Shirin Taba Ka Lashe.
-
Taba Ka Lashe
16/11/2021 Duração: 09minWurin da ake tsugune da daruruwan mata da ake zargi da aikata maita a wata cibiya ta musamman da ake wa lakabi da "Sansanin mayu” a arewacin Ghana.
-
Taba Ka Lashe: 27.10.2021
02/11/2021 Duração: 09minA duk ranakun 12 ga watan Rabi'ul Auwal na ko wacce shekara, al'ummar Musulmi a fadin duniya kan yi bukukuwan tunawa da ranar haihuwar Manzon Allah Annabi Muhammad (SAAW). A wannan shirin mun yi nazarin yadda aka gudanar da bukukuwan na bana a jihar Kano da ke Najeriya.
-
Taba Ka Lashe 22.09.2021
28/09/2021 Duração: 09minYadda zamani ke shirin gusar da al'adun gargajiyan jahar Gaya a jamhuriyar Nijar. Latsa kasa don jin cikakken shirin.
-
Taba Ka Lashe: 15.09.2021
21/09/2021 Duração: 10minAmfani da ahnnun hagu, halitta ce da daga Allah. Sai dai wasu na fuskantar kalubale sakamkon wasu al'adu da ma addinai. Ku saurari shirinmu na Taba Ka Lashe.
-
Taba Ka Lashe: 01.09.2021
07/09/2021 Duração: 09minKo kun san yadda kabilar Igbo da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, ke bikin binne gawa? Shirin Taba Ka Lashe.
-
Taba ka lashe 04.05.21
31/08/2021 Duração: 09minAl'adar wasan kara a yankin Damagaram na Jamhuriyar Nijar wanda matasa ke yi a lokacin kaka bayan girbin amfani gona
-
Taba Ka Lashe: 11.08.21
24/08/2021 Duração: 10minKo kun san cewa akwai fadar Hauasawa har ma da sarkinsu a Turai? Shirin Taba Ka Lashe ya yi nazari kan batun wannan sarauta.
-
Taba Ka Lashe: 04.08.2021
10/08/2021 Duração: 09minKo kuna da masaniya kan yadda al'adar wasan kara ke gudana a jihar Damagaram da ke Jamhuriyar Nijar? Shirin Taba Ka Lashe
-
Taba Ka Lashe: 21.07.2021
27/07/2021 Duração: 09minShadi, dadaddiyar al'ada ce ta Fulani da aka fi amfani da ita wajen neman aure. Sai dai a yanzu al'amura sun sauya. Ko ya al'adar ta shadi take gudana a yanzu? Shirin Taba Ka Lashe.
-
Taba ka Lashe 21.07.2021
20/07/2021 Duração: 09minAl'adar Sharo na fulani wata dadaddiyyar al'ada ce mai muhimmanci ga fulani wacce tun shekaru masu yawa suke yin ta musamman domin hada aure tsakanin samari da yan mata.
-
Taba Ka Lashe: 07.07.2021
13/07/2021 Duração: 09minKo kun san irin baiwar da aka yi ittifakin cewa 'yan tagwaye ko kuma 'yan biyu na da su a kasashen Hausa masu tarin al'adu? Shirin Taba Ka Lashe.
-
Taba Ka Lashe: 30.o6.2021
06/07/2021 Duração: 09minJamhuriyar Nijar na fuskantar tarin matsaloli a fannin shirya fina-finai, sai dai tuni aka dauki mataki domin shawo kan wadannan matsaloli.
-
Taba Ka Lashe: 23.06.2021
29/06/2021 Duração: 09minShirin na wannan lokaci, ya yi nazari ne kan taron 'yan jaridu na duniya da tashar DW ta saba shiryawa duk shekara, wato Global Media Forum.
-
Taba Ka Lashe: 16.06.2021
22/06/2021 Duração: 09minBikin nadin fadawan masarautar Tsibiri, cikin gundumar Dogon Doutchi da ke Jamhuriyar Nijar. Shin ya bikin ke gudana? Shirin Taba Ka Lashe.
-
Taba Ka Lashe: 19.05.2021
25/05/2021 Duração: 09minAl'adar hawan kaho a Jamhuriyar Nijar, dadaddiyar al'ada ce ta ake gudanar wa a karshen watan azumin Ramadana na kowacce shekara. Ku biyo mu domin jin yadda al'adar take.
-
Taba Ka Lashe 14.04.2021
20/04/2021 Duração: 09minDinke baraka bayan cika shekaru 30 da aukuwar wani rikici mai nasaba da kabilanci a jihar Bauchi da ke Najeriya wanda ya salwantar da rayukan jama'a masu tarin yawa.
-
Taba Ka Lashe: Zamantakewar Yarbawa da Hausawa
13/04/2021 Duração: 09minShirin yayi nazari kan zamantakewar Fulani da Hausawa tun bayan fuskantar barazana ta asarar rayuka da dukiya a wasu jihohin kudu maso yammacin Najeriya.