Sinopse
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Episódios
-
Alhaji Adamu Muhammad Madawa kan rashin maida mulki hannun farar hula a Nijar
20/11/2024 Duração: 03minKusan shekara guda da rabi da juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar, har ya zuwa yanzu babu wani shiri daga sojojin na mayar da mulki ga fararen hula. Wannan ya sa wasu daga cikin jama'ar ƙasar gabatar da buƙata ga sojoji da su sake tunani akai domin bai wa jama'a damar zaɓin shugabannin da suke so. Domin tattauna wannan batu, Bashir Ibrahim Idris ya tintibi Alhaji Adamu Muhammad Madawa, daya daga cikin shugabannin ƴan Nijar mazauna Najeriya. Ku latsa alamar sauti dominjin yadda zantawarsu ta gudana........
-
Malam Hussaini Manguno kan ziyarar da tawagar Najeriya ta kai Chadi
19/11/2024 Duração: 03minTawagar gwamnatin Najeriya ta ziyarci ƙasar Chadi, inda ta gana da shugaban kasa Mahamat Idris Deby sakamakon barazanar da ya yi na janye dakarunsa daga rundunar hadin gwuiwar dake yaki da boko haram. Tawagar a ƙarƙashin Malam Nuhu Ribadu, ta kunshi hafsan tsaron Najeriya Janar Christopher Musa. Bayan ganawar Bashir Ibrahim Idris ya tatatuna da masanin harkar tsaro Malam Hussaini Manguno. Ku latsa alamar sauti don sauraron yadda zantawarsu ta gudana........
-
Dr Isa Abdullahi kan inganta alakar kasuwanci tsakanin Najeriya da India
18/11/2024 Duração: 03minA karshen makon da ya gabata ne Firaministan India Narendra Modi ya ziyarci Najeriya domin inganta dangantakar ƙasashen biyu musamman a ɓangaren kasuwanci. Alkaluma sun bayyana cewar kamfanonin India sama da 200 sun zuba jarin da ya zarce dala biliyan 27, yayin da Modi ke goyan bayan Najeriya wajen ganin ta zama mamba a kungiyar G20 da BRICS. Dangane da ziyarar Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziki, Dr Isa Abdullahi. Ku latsa alamar sauti domin jin yadda zantawarsu ta gudana............
-
Ambasada Abubakar Chika kan buƙatar ƙorar Isra'ila daga Majalisar Ɗinkin Duniya
14/11/2024 Duração: 03minShugabannin ƙasashen Musulmi da na Larabawa, sun kammala taronsu da gabatar da buƙatar korar Isra'ila daga Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma gudanar da bincike mai zaman kansa kan kisan gillar da ta yi a Gaza. Taron ya kuma amince da wasu ƙudurori daban daban da su kai ga tabbatar da ƙasar Falasɗinu. Dangame da matakan da shugabannin suka ɗauka, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ambasada Abubakar Chika, tsohon jakadan Najeriya a Iran. Ku latsa alamar sauti don jin cikakkiyar tattaunawar ta su..........
-
Alhaji Muhammadu Magaji kan saye kayan amfanin gona a Najeriya
13/11/2024 Duração: 03minMazauna yankin arewacin Najeriya na bayyana damuwa kan yadda kamfanoni da ƴan kasuwa ke rige rigen sayen kayan abinci a hannun manoma. Masana na bayyana fargabar cewar matakin zai sanya kayan abincin ya yi tsada a daidai lokacin da jama'a ke fama da tsadar rayuwa. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Alhaji Muhammadu Magaji, Sakataren tsare tsare na ƙungiyar manoman Najeriya dangane saye kayan abincin. Ku latsa alamar sauti don jin cikakkiyar tattaunawar ta su........
-
Tattaunawa da Abdullahi Idris Zuru kan harin Lakurawa a jihar Kebbi
11/11/2024 Duração: 03minSabuwar ƙungiyar ta’addanci ta Lakurawa da ta bayyana a makwannin baya-bayan nan cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya ta hallaka aƙalla mutane 15 a harin da ta kai garin Mera na jihar Kebbi baya ga kora tarin dabbobin jama’a.Bayanai sun ce an yi artabu tasakanin yan ta’addan da mutanen gari gabanin tserewarsu. Dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da kakakin gwamnatin jihar kebbi Abdullahi Idris Zuru wanda ya bayyana cewa tuni gwamnati ta ɗauki matakan baiwa jama'a kariya baya ga aikewa da twaga don bin sahun ƴan ta'addan.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.
-
Farfesa Bello Bada kan bullar sabuwar kungiyar ta'addanci a Najeriya
08/11/2024 Duração: 03minRundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da samun wata sabuwar kungiyar 'yan ta'adda da ake kira Lakurawa a Jihohin Sokoto da Kebbi wadanda aka ce sun fito ne daga kasashen mali da Libya da kuma Jamhuriyar Nijar. Rahotanni sun ce 'yayan wanan kungiya na sanya haraji da kafa dokoki a yankunan da suke.Dangane da wannan sabon al'amari, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Bello Bada na Jami'ar Usman Dan Fodio dake Sokoto.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
-
Sule Ammani kan abin da ya biyo bayan nasarar ƙubutar da yaran arewacin Najeriya
06/11/2024 Duração: 03minGa dukkan alamu matsalar da ta biyo bayan kama ƙananan yaran da ƴan sandan Najeriya su ka yi lokacin zanga-zangar tsaɗar rayuwa a Kano ta zaburar da wasu daga cikin shugabannin yankin kan bukatar haɗa kai domin ceto arewacin ƙasar daga halin da ya samu kansa, bayan sakin yaran, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da ɗaya daga cikin dattawan yankin Alhaji Sule Ammani Yarin Katsina.
-
Farfesa Shehu Abdullahi Zuru kan tasirin zaɓen Amurka ga Duniya
05/11/2024 Duração: 03minYau Amurkawa ke kaɗa ƙuri'a a zaɓen ƙasar da bayanai ke cewa fiye da mutum miliyan 180 za su jefa ƙuri'unsu don zaɓen guda cikin ƴan takara biyu da ke fafatawa wato tsohon shugaban ƙasar Donald Trump na jam'iyyar Republican da Kamala Harris ta Jam'iyyar Democrat wadda mataimakiyar shugaban ƙasa ce kuma ƴar takarar mace baƙar fata ta farko a tarihin ƙasar. Domin jin tasirin wannan zaɓe da ya ɗauki hankalin duniya Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Shehu Abdullahi Zuru na Jami'ar Baze.
-
Farfesa Shehu Abdullahi Zuru kan tasirin zaɓen Amurka ga Duniya
05/11/2024 Duração: 03minYau Amurkawa ke kaɗa ƙuri'a a zaɓen ƙasar da bayanai ke cewa fiye da mutum miliyan 180 za su jefa ƙuri'unsu don zaɓen guda cikin ƴan takara biyu da ke fafatawa wato tsohon shugaban ƙasar Donald Trump na jam'iyyar Republican da Kamala Harris ta Jam'iyyar Democrat wadda mataimakiyar shugaban ƙasa ce kuma ƴar takarar mace baƙar fata ta farko a tarihin ƙasar. Domin jin tasirin wannan zaɓe da ya ɗauki hankalin duniya Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Shehu Abdullahi Zuru na Jami'ar Baze.
-
Attahiru Bafarawa kan tsare yaran arewacin Najeriya saboda zanga zanga
04/11/2024 Duração: 03minƘungiyar Amnesty International a Najeriya tare da wasu ƙungiyoyin kare hakkin Bil Adama da kuma wasu fitattun ƴan ƙasar sun bayyana damuwa dangane da yadda rundunar ƴan sandan ƙasar ta gurfanar da wasu yaran da suka fita hayyacinsu a gaban kotu, inda ake tuhumarsu da zanga zangar neman kifar da gwamnati. Rahotanni sun ce ministan shari’a ya bukaci mika masa takardun shari’ar wadda ta haifar da cece kuce a fadin ƙasar. Kan haka Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da ɗaya daga cikin dattawan arewacin Najeriya, kuma tsohon Gwamnan Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana a kai.
-
Halin da masana'antun arewacin Najeriya ke ciki na rashin wutan lantarki
31/10/2024 Duração: 03minMasu masana'antu a arewacin Najeriya sun bi sahun sauran jama'ar yankin wajen bayyana damuwarsu a kan halin da suka samu kansu na rashin wutan lantarki sama da kwanaki goma. Kan haka Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da mataimakin shugaban ƙungiyar masu masana'antu ta ƙasa MAN, Ali Safiyanu Madugu.
-
Farfesa Shehu Abdullahi Zuru game da binciken wasu alkalai a jihar Rivers
30/10/2024 Duração: 03minBabbar mai shari'a a Najeriya tare da Hukumar Kula da Ayyukan Shari'a ta NJC sun kaddamar da bincike a kan yadda wasu alkalai a jihar Rivers suka dinga bada hukunce hukunce da ke karo da juna dangane da zaben kananan hukumomin da aka yi a jihar. Wannan umarni na zuwa ne bayan an samu irin wannan matsala a jihar Kano. Saboda haka Bashir Ibrahim Idris ya tintibe masanin ɓangaren shari'a Farfesa Shehu Abdullahi Zuru na jami'ar Baze dake Abuja. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana.........
-
Murtala Aliyu kan matsayar ACF na rashin wutar lantarki a Arewacin Najeriya
29/10/2024 Duração: 03minƘungiyar Tintiba ta Arewacin Najeriya da ake kira ACF, ta bi sahun wasu jama'ar yankin wajen bayyana damuwarta kan matsalar rashin wutar da ake fuskanta na sama da mako guda a yankin, inda ta buƙaci shugaban ƙasar da ya kafa dokar ta ɓaci a kan lamarin. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Sakataren kungiyar, Malam Murtala Aliyu, wanda tsohon ministan wutar lantarki ne a ƙasar Ku latsa alamar sauti don sauraron yadda zantawarsu ta gudana........
-
Alhaji Sule Ammani Yarin Katsina kan rashin wutar lantarki a Arewacin Najeriya
28/10/2024 Duração: 03minMazauna yankin Arewacin Najeriya sun kwashe kwanaki 7 ba tare da hasken wutar lantarki ba, abinda ya yi sanadiyar durkushewar jama'a musamman masu sana'oin da suka dogara ga wutar. Wannan matsala na barazana ga rayuwa da kuma tattalin arzikin yankin. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da daya daga cikin dattawan yankin, Alhaji Sule Ammani Yarin Katsina. Ku latsa alamar sauti don jin cikakkiyar zantawarsu ta su........
-
Dokta Abbati Baƙo kan taron BRICS da ake yi a Rasha
24/10/2024 Duração: 03minShugaban Rasha Vladimir Putin ya ce taron kasashen BRICS dake gudana a kasarsa zai duba yiwuwar samar da wata sabuwar tafiya wadda za ta yi gogaggaya da wadda ake amfani da ita a duniya yanzu haka.Akalla shugabannin kasashe 30 ke halartar taron a birnin Kazan.Domin tasirin wannan kungiya ta BRICS dake Shirin kawo sauyi a duniya, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Abbati Bako masanin siyasar duniya, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
-
Dr Yahuza Ahmad Getso kan fargabar kwararar ƴan ta'adda zuwa jihar Kano
22/10/2024 Duração: 03minWani sabon rahoton binciken kwakwaf da aka gudanar ya bankado yadda ‘yan ta’adda daga jihohin Zamfara, Sokoto, Katsina da kuma Kaduna ke tsallakawa jihar Kano domin samun mafaka. Jihar Kano ce dai ke da dama-dama ta fannin ingancin tsaro a jihohin arewa maso yammacin Najeriya.Shin yaya masana ke kallon wannan sabon salo da kuma hatsarin da yake da shi, Rukayya Abba Kabara ta tattauna da Dr Yahuza Ahmad Getso masanin tsrao a Najeriya, ga kuma yadda tattaunawar tasu ta kasance.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar......
-
Dr Kasum Garba Kurfi game da yabawa tsarin tattalin arzkin Najeriya da bankin duniya yayi
21/10/2024 Duração: 03minBankin duniya ya yaba da sauye sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Najeriya ke aiwatarwa, tare da bai wa hukumomin ƙasar shawarar kar su kuskura su koma da baya. Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da talakawan ƙasar ke kokawa saboda ƙuncin rayuwa. Dangane da wannan matsayi Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziki Dr Kasum Garba Kurfi. Ku latsa alamar sauti don jin cikakkiyar zantawarsu..............
-
Sojojin Nijar sun gaza a yaƙi da rashawa - Transparency International
18/10/2024 Duração: 03minƘungiyar Transparency International da ke yaƙi da cin hanci da rashawa, reshen Jamhuriyar Nijar ta fitar da wani sabon rahotoda ke zargin sojojin ƙasar da gazawa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma hana fararen hula guraben shugabancin hukumomin gwamnati. Dangane da wannan zargi, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shugaban Transparency International, reshan Nijar, Mamman Wada.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu.
-
Kaften Isa Usman: Halin da shugaba Paul Biya na Kamaru ke ciki
11/10/2024 Duração: 03minYayin da tababa da rashin tabbas suka mamaye halin da shuhgaban Kamaru Paul Biya ke ciki, gwamnatin ƙasar ta haramta wa kafofin yaɗa labarai sharhi dangane da shugaban. A kan wannan batu ne, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da kaften Isa Usman, tsohon dogarin Ahmadou Ahidjou da kuma shi kansa Paul Biya.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu.