Wasanni

Informações:

Sinopse

A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.

Episódios

  • Nazari kan yadda wasannin kwata finals na gasar zakarun Turai su ka gudana

    22/04/2024 Duração: 09min

    Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya maida hankali ne kan yadda wasannin matakin kwata finals na gasar zakarun Turai su ka gudana. A makon da ya gabata ne dai aka kammala wasannin zagayen, inda aka fafata a wasanni 4. Dortmund da aris Saint-Germain da Bayern Munich da Real Madrid ne suka kaiga wasan kusa da na karshe a gasar ta bana. A yanzu Bayern Munich zata fafata da Real Madrid ita kuwa Borussia Dortmund ta kara Paris Saint-Germain.Ku letsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh.......

  • Hasashen yadda za ta kaya a gasar Firimiyar Ingila

    15/04/2024 Duração: 09min

    Shirin a wannan lokaci ya fi karkata akalar ne kan gasar Firimiyar Ingila, wadda ke ci gaba da jan hankali, duk da shawo gangarar da akayi. Yar manuniyar dai tuni ta fada kan kungiyoyin ukun saman tebur, wato Manchester City, Arsenal da Liverpool, lura da yadda suke kan kan kan a yawan maki, abunda ke kara nunawa duniya yadda gasar ta Firimiya ta ke ci gaba da jan zarenta a fagen tamola.Ko da yake a halin yanzu Manchester City ce ta karbe ragamar teburin wannan gasa, bayan rashin nasarar da Arsenal da kuma Liverpool suka samu a nasu wasannin.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Khamsi Saleh.

  • Shiri na musamman kan shirye-shiryen gasar Olympics kashi na 2

    08/04/2024 Duração: 09min

    A wannan makon Shirin Duniyar Wasanni ya yi duba ne kan yadda ake tufka da warwara game da tsarin tsaro a lokacin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics da birnin Paris zai karbi bakunci a watan Yulin wannan shekarar. Shire-shiryen gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta Olympics da birnin Paris na Faransa zai karbi bakunci a watan Yuli mai zuwa sunyi nisa, domin dai rahotanni na nuna cewar an kammala tanadin kusan dukkanin inda za a gudanar da wadannan wasanni.Sai dai wani hanzari ba guda ba, duk da matakan da kasar ta Faransa ta dauka na tabbatar da tsaron ‘yan wasa da kuma na ‘yan kallo, bayanai na nuna cewar akwai alamun fuskantar barazanar tsaro a lokacin gasar.Wannan lamari dai ya biyo bayan harin ta’addancin da aka kai birnin Moscow wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 140.A lokacin wata zantawa da aka yi shugaban Faransa Emmanuel Macron a makon da ya gabata, ya ce babu shakka, akwai yuwuwar Rasha za ta kai hari a lokacin gasar da ke tafe.Kai hari a lokacin gasar OlympicsKai hari a yayi gasar guj

  • Sharhi game da kamun ludayin Finidi George a tawagar Super Eagles

    01/04/2024 Duração: 09min

    Shirin a wannan mako shirin ya yi sharhi ne kan kamun ludayin mai rikon kwaryar tawagar Super Eagles ta Najeriya Finidi George, bayan da tawagar ta buga wasannin sada zumunci biyu a makon daya gabata karkashin kulawar Finidi George da aka damkawa tawagar a hannunsa a matsain mai horaswa na rikon kwarya. Tawagar ta yi nasara kan takwararta ta Ghana a wasan farko da tayi, sai dai kuma ta sha kashi a hannun Mali karo na farko cikin gwamman shekaru da hakan ta faru.Ku latsa alamar sauti donjin cikakken shirin tare da Khamis Saleh......

  • Masar ce ta daya a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta Afrika da aka yi a Ghana

    25/03/2024 Duração: 09min

    Shirin Duniyar Wasanni a wannan mako yayi duba ne kan yadda gasar guje-guje da tsalle -tsalle ta nahiyar Afrika ta gudana a kasar Ghana. Kasar Masar ce ta zamo zakarar lashe lambobin yabo har 189, sai Najeriya da ke bi mata da lambobn yabo 120, yayinda Janhuriyar Nijar ta lashe lambobin yabo 11, lamarin da ya bata damar zama amatsayi na 16 a teburin kasashe 53 da suka halarci gasar bayan da Cape Verde ta janye daga fafatawa a wannan karon. Wannan ne kuma  karo na 13 da ake gudanar da wannan gasa a tarihi, inda aka gudanar da wasanni kusan 30.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.....

  • Sharhi kan yadda wasannin kwata finals na gasar zakarun Turai za su gudana

    18/03/2024 Duração: 09min

    Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya maida hankali ne kan yadda wasannin matakin kwata finals na gasar zakarun Turai za su gudana. A ranar Juma’ar da ta gabata ce dai hukumar kula da wasan kwallon kafar Turai UEFA ta hada yadda kungiyoyi 8 da suka yi saura a gasar zakarun Turai z asu kara da junanansu. Tsohon kyaftin din Najeriya wanda kuma ya taba lashe gasar da kungiyar Chelsea Mikel John Obi ne ya jagoranci hada yadda kungiyoyin za su kara da juna. Arsenal za ta fafata da Bayern Munich, Atletico Madrid za ta kece raini da Borussia Dortmund, Real Madrid ta kara da Manchester City ya yin da Paris Saint-Germain za ta kara da Barcelona.Ku letsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh.......

  • Ci gaban da aka samu a wasan damben gargajiya a Najeriya

    11/03/2024 Duração: 09min

    Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon tare da Khamis Saleh ya maida hankali ne kan irin ci gaban da aka samu a bangaren wasan damben gargajiya a Najeriya.

  • Yadda aka kammala zangon farko na gasar kwallon kafa ta Firimiyar Najeriya

    04/03/2024 Duração: 10min

    Shirin awanan lokaci zai nazari game da yadda zangon farko na gasar Firimiyar Najeriya ya kammala, inda tuni aka juya zagaye na biyu na gasar ta kwararru.Shirin ya kuma duba batun soma gasar a kan lokaci da kuma batun daukar nauyi, sai kuma batun rashin ingancin filaye, baya ga kuma karanchin samun bayanan ‘yan wasan da ke taka leda a gasar.Latsa alamar sauti don sauraron shirin: 

  • Nazari kan komawar Kylian Mbappe kungiyar Real Madrid a kaka mai zuwa

    26/02/2024 Duração: 09min

    Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya yi nazari ne kan komawar dan wasan gaba na kungiyar PSG, Kylian Mbappe  kungiyar Real Madrid a karshen kakar bana. Yanzu dai za a iya cewa an yi ta, ta kare bayan da a ranar 13 ga wannan watan ne dan wasan mai shekara 25 ya sanar da kungiyarsa PSG batun sauya shekarar tasa da zarar kwantiraginsa ya kare a karshen kakar watan Yuni. Kungiyar Real Madrid dai tayi suna wajen dauko manyan ‘yan wasan da tauraruwarsu ke haskawa a fagen kwallon kafa a duniya, ba tare da la'akari da tsadarsu ba.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.....

  • Yadda aka gudanar da gasar Polo ta bana a garin Jos

    19/02/2024 Duração: 09min

    Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya mai da hankali ne kan yadda aka gudanar da gasar Polo a Jahar Filato da ke arewacin Najeriya. A wannan karo, club club din wasan kwallon dawakin da suka fafata a gasar sun fito ne daga jihohin Lagos, Nasarawa, Bauchi, Taraba, Kaduna, Kano, Niger da kuma Katsina. A karshe dai club din Keffi Ponies ta jihar Nasarawa ta lashe gasar a karawar karshe da suka yi da Malconmines  daga  Filato mai masaukin baki. Ku latsa alamar suti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......

  • Yadda Ivory Coast ta lashe kofin AFCON bayan ta doke Najeriya

    12/02/2024 Duração: 09min

    A daren jiya Lahadi ne aka kammala gasar lashe kofin Afrika AFCON karo na 34 da Ivory Coast ta karbi baukunci kuma daga bisa ta lashe gasar. Najeriya ce ta fara zura kwallon farko ta hannun William Ekong tun kafin a tafi hutun rabin lokacin, sai dai bayan dawowa ne tawagar ta Elephants ta farke ta hannun Kesse kafin daga bisani a minti na 81 ta kara kwallo ta hannun Sebestin Hallar wacce ta bata nasara. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin tare da Khamis Saleh

  • Mai masaukin baki Ivory Coast ta lashe kofin AFCON bayan doke Najeriya

    12/02/2024 Duração: 09min

    Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh, ya mayar da hankali ne kan yadda ta kaya a wasan karshe na cin kofin AFCON wanda Ivory Coast mai masaukin baki ta lashe bayan doke Najeriya da kwallaye 2 da 1. Shirin ya yi bitar muhimman batutuwan da ke kunshe a gasar a tsawon makwanni 3 da aka shafe ana fafatawa tsakanin kasashe 24.Sai kuma batun tagomashin da kasashen da suka zo na daya da na biyu da kuma na 3 za su samu.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.....

  • Yadda wasannin zagayen Kwata final suka kaya a gasar AFCON

    05/02/2024 Duração: 10min

    Shirin 'Duniyar  Wasanni' na wannan lokacin yayi nazari ne akan wasannin matakin dab da na kusa da na karshe wato na zagayen Kwata final da aka yi a gasar AFCON.  Yanzu haka dai kasashe hudu ne suka rage a gasar ta cin kofin kasashen nahiyar Afirka da kasar Ivory Coast ke karbar bakunci, bayan wasannin da aka fafata a ranakun Juma’a da Asabar.

  • Matakin zagayen dab da na kusa da na karshe a gasar lashe kofin Afrika AFCON

    02/02/2024 Duração: 09min

    A yau Juma’a nan ce dai za a fara buga wasannin zagen dab da na kusa da na karshe a gasar lashe kofin Afrika AFCON da ke gudana a kasar Ivory Coast.Za kuma a fara karawar ne tsakanin Najeriya da Angola karfe shida agogon Najeriya, kafin da misalign karfe 9 a buga wasa tsakanin DR Congo da Guinea.A wasannin gobe Asabar, akwai karawa tsakanin Mali da Cote d’Ivoire sai kuma Cape Verde da Afrika ta Kudu.

  • Nazari kan karawar da aka yi tsakanin Najeriya da Kamaru a gasar AFCON 2023

    29/01/2024 Duração: 10min

    A ranar asabar ne dai aka fafata tsakanin tawagar Super Eagels ta Najeriya ta tawkararta ta Indomitable Lions ta Kamaru, a wasan zagayen ‘yan 16 a gasar lashe kofin Afrika AFCON da Ivory Coast ke karbar bakunci.Wannan wasa dai ya ja hankali a wannan gasa, ganin yadda kasashen biyu ke da suna a fagen kwallon kafar Afrika, sannan kuma akwai dadaddiyar hamayya a tsakaninsu.

  • Najeria da Kamaru za su fafata a zagaye na 2 na gasar AFCON

    26/01/2024 Duração: 09min

    Najeriya karkashin  mai horar da kungiyar Jose Peseiro za ta nemi kare maratabar ta da kuma neman ganin ta tsallaka mataki na gaba a wanan gangami,yayida a daya wajen ,Kamaru  a cewar mai horar da ita ,Rigobert Song za su kasance a kan bakar su na ganin su doke Najeriya. A tarihi,haduwar wadanan kungiyoyi Najeriya da Kamaru a shekaru baya suka kasance gagara badau a fagen tamola, Najeriya da Kamru sun hadu sau 22.,Najeriya ta samu nasara a wasanni 11 da ta buga da Kamaru. Yayin da Kamaru ta samu galaba a kan Najeriya sau  hudu Kungiyoyin biyu sun yi canjaras sau bakwai. A tarihin lashe kofin gasar Afirka na kwallon kafa baya ga Masar,da ta lashe Kofin sau 7,Kamaru ta daga wannan kofi sau 5 sai Ghana sau 4.   A bangaren Najeriya,kungiyar Super Eagles ta lashe kofin sau uku, shekarar 1980,1994 sai 2013..Khamis Saley a cikin wannan shiri na Duniyar wasanni,ya mayar da hankali a gasar.

  • Yadda kasashe ke bayar da mamaki a wasannin gasar AFCON a Ivory Coast

    22/01/2024 Duração: 09min

    Shirin duniyar wasanni tare da Khamis Saleh ya mayar da hankali kan yadda gasar AFCON ke ci gaba da gudana a Ivory Coast, gasar da zuwa yanzu aka kammala zagaye biyu na matakin rukuni. Gasar ta AFCON a bana ta zo da wani yanayi ta yadda kasashen da ba a tsammanin su iya kai labari ke ci gaba da bayar da mamaki, yayinda wasu manyan kasashe kuma a fagen tamaular nahiyar suka kasa katabus.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin..

  • Yadda aka kammala wasannin farko na rukuni a gasar AFCON

    19/01/2024 Duração: 09min

    Shirin "Duniyar Wasanni" a wannan lokaci zayyi duba ne akan yadda aka kammala wasannin farko na matakin rukuni da kuma yadda aka faro na biyu a gasar AFCON da ke gudana a Ivory Coast. An kuma fara wasannin ne da karawar da aka yi tsakanin Equatorial Guinea Guinea-Bissau, inda Equatorial Guinea ta samu nasara akan Guinea-Bissau da ci 4-2. Sai kuma wasa na biyu da aka yi a rukunin na A tsakanin Najeriya da Ivory Coast mai masaukin baki, kuma kwallo daya mai ban haushi da zura tawagar Super Eagles ta Najeriya ta zura ta hannun William Troost-Ekong ce ta bada nasara a wasan.Wannan nasara ta farko da Super Eagles ta samu a rukunin A, ta farfado da fatan Najeriya na kai wa zagaye na biyu a gasar lashe kofin Afrika, yayinda ita kuwa Ivory Coast hannun agogo ya koma mata baya.Ku lastsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.......

  • Gasar cin kofin kasashen Afirka ta kankama a Ivory Coast

    15/01/2024 Duração: 09min

    A ranar asabar da ta gabata ne aka fara gasar lashe kofin nahiyar Afrika wato AFCON da kasar Ivory Coast ke karbar bakunci. Wannan ne karo na 34 da ake gudanar da wannan gasa, kuma kasashe 24 zasu fafata a matakin rukuni.

  • Yadda aka daina bai wa matasan 'yan wasan Najeriya dama a Super Eagles

    29/12/2023 Duração: 09min

    Shirin a wannan mako ya mayar da hankali ne ga batun yadda ake korafin rashin amfani da ‘yan wasan gida a tawagar babbar kungiyar kwallon kafa ta Najeriya. Sabanin a baya, da hukumar kwallon kafa ta Najeriyar, kan shirya wasanni na musamman domin fitar da 'yan wasan da za ta yi amfani da su wajen wakiltar kasar a manyan wasanni.Kan wannan kalubale ne Khamis Saleh ya tattauna da masana a fannin kwallon kafa.Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.

Página 1 de 2