Sinopse
Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu
Episódios
-
Ra'ayoyin masu saurare kan kifar da gwamnatin Al-Assad na Syria
10/12/2024 Duração: 09minA ƙarshen makon da ya gabata ne ƴan tawaye suka kifar da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad na Syria da zuri’arsa suka shafe shekaru 50 su na mulki a ƙasar. Rahotanni dai na cewa Al-Assad da iyalansa sun tsere daga ƙasar inda ake kyautata zaton cewa Rasha ta basu mafaka, lamarin da ƙasar Rashan ta musanta, yayin da ƙasashen duniya ke tofa albarkacin bakinsu.Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin tare da Hauwa Aliyu..
-
Ra'ayoyin Masu Saurare kan zaɓen Ghana
09/12/2024 Duração: 09minMataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar jam’iyya mai mulki a Ghana, Mahamudu Bawumia ya amince da shan kaye a zaɓen ƙasar, inda ya taya tsohon shugaban ƙasa John Mahama murnar lashe zaɓen. Wannan ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasar da aka yi a Asabar ɗin ƙarshen mako 7 ga watan Disamba, wanda rahotanni suka tabbatar da cewa ya gudana cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.Shin ya ku ka kalli yadda zaɓen na Ghana ya gudana?Me za ku ce kan yadda Bawumia ya amince da shan kaye tun kafin a fitar da sakamakon zaɓen?Wane darasi ku ke ganin ƴan siyasa a yankunanku za su koya daga zaɓen Ghana?Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin
-
Ra'ayoyin masu saurare kan caccakar tsarin zaɓen Kamaru
06/12/2024 Duração: 09minA Jamhuriyar Kamaru, wani babban limamin cocin Katolika a Duwala, Archbishop Samuel Kleda ya caccaki tsarin zaben ƙasar, wanda ya ce an tsara shi ne don bai wa shugaba mai ci damar ci gaba da yin kane-kane kan madafun iko, yana mai cewa akwai buƙatar gyara in dai dimokaradiyyar ake so. Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi...
-
Ra'ayoyin masu sauraro kan kame mafi girma da EFCC ta yi a Najeriya
04/12/2024 Duração: 09minA Najeriya, kwanan nan ne kotu ta karbe wani rukuni mai ƙunshe da gidaje 753 mallakin wani tsohon gwamnan babban bankin ƙasar, nasara mafi girma da hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati ta taɓa samu a cikin sama da shekaru 21 da kafuwarta. Wannan shi ne maudu’in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a yau. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin tare da Oumaru Sani:
-
Ra'ayoyin masu sauraro kan ranar masu buƙata ta musamman ta duniya
04/12/2024 Duração: 10minKamar yadda aka saba, RFI Hausa na bai wa masu saurare damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwa da dama da ke ci musu tuwo a kwarya. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware ranar 3 ga watan Disambar kowacce shekara a matsayin ranar masu buƙata ta musamman, wato mutane da ke rayuwa da wata naƙasa a fadin duniya.Wannan shi ne maudu’in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a yau.Ku latsa alamar sauti domin sauraren shirin tare da Hauwa Halliru Gwangwazo:
-
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa da dama
29/11/2024 Duração: 10minKamar yadda aka saba, RFI Hausa na bai wa masu saurare damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwa da dama da ke ci musu tuwo a kwarya. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a
-
Kan ficewar Nijar, Mali, Burkina Faso daga ECOWAS
21/11/2024 Duração: 10minA watan Janairun shekarar da ta gabata Jamhuriyar Nijar da wasu ƙasashen Sahel 3 su ka bayyana aniyar ficewa daga ƙungiyar ECOWAS ta ƙasashen yammacin nahiyar Afrika a hukumance. A halin da ake ciki, watanni 3 ne kacal su ka rage wa’adin ficewar su ta cika, bayan sanar da ECOWAS batun janyewar kamar yadda dokokinta su ka tanada.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
-
Kan yadda 'yan bindiga suka kone amfanin gonar da aka girbe a arewacin Najeriya
14/11/2024 Duração: 10minA Najeriya a yayin da aka fara girbin amfanin gona, rahotanni daga sassan ƙasar sun bayyana yadda hukumomi, kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane ke sayen ɗimbim hatsi su na tarawa, lamarin da ya haddasa tsadar su jim kaɗan bayan da farashi ya fara saukowa. A cewar masu lura da al’amura, wannan lamari zai ta’azzara tsadar kyayyakin abinci, ganin ayyukan ƴan bindiga su ka hana al’ummomi da dama yin noma.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
-
Kan yadda kamfanoni ke saye amfanin gonar da aka girbe a Najeriya
13/11/2024 Duração: 09minA Najeriya a yayin da aka fara girbin amfanin gona, rahotanni daga sassan ƙasar sun bayyana yadda hukumomi, kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane ke sayen ɗimbim hatsi su na tarawa, lamarin da ya haddasa tsadar su jim kaɗan bayan da farashi ya fara saukowa. A cewar masu lura da al’amura, wannan lamari zai ta’azzara tsadar kyayyakin abinci, ganin ayyukan ƴan bindiga su ka hana al’ummomi da dama yin noma.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa da dama
08/11/2024 Duração: 10minKamar yadda aka saba, RFI Hausa na bai wa masu saurare damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwa da dama da ke ci musu tuwo a kwarya. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a
-
Ko meke haifar da tarnaƙi a tabbatar da tsaro a arewacin Najeriya?
22/10/2024 Duração: 04minRa'ayoyin masu saurare na wannan rana ya mayar da hankali kan yadda aka kwashe watanni biyu bayan da shugaban kasa ya umarci hafsoshin tsaro da su tare a jihar Sokoto don tabbatar da tsaro, amma har yanzu 'yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare ba kakkautawa. Shin ko me ke haifar da tarnaki ga kokarin tabbatar da tsaro a arewacin Najeriya?Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna
-
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa da dama
18/10/2024 Duração: 10minKamar yadda aka saba, RFI Hausa na bai wa masu saurare damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwa da dama da ke ci musu tuwo a kwarya. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a
-
Ra'ayoyi: Najeriya za ta shafe shekara 100 kafin magance talauci
17/10/2024 Duração: 10minBankin Duniya, ya ce Najeriya da wasu ƙasashe da dama masu tasowa, za su iya shafe tsawon shekara ɗari a nan gaba kafin su yi nasarar rage kaifin talauci da ke addabar al’ummominsu. Wannan gargaɗi na Bankin Duniya na zuwa ne a daidai lokacin da bayanai ke cewa kusan a kowace rana ta Allah ana samun karuwar mutanen da suka dogara da malauna ne domin samun abin da za su ci da kuma iyalansu.Shin, ko yaya za ku bayyana matsayin talauci ko fara a inda ku ke rayuwa?Ko kun gamsu da irin matakan da hukumomin ƙasashen ke ɗauka domin rage kaifin talauci a tsakanin al’umma?Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin
-
Ra'ayoyin masu saurare kan kaurace wa karawa da Libya da tawagar Najeriya ta yi
15/10/2024 Duração: 10minShirin ra'ayoyin masu sauraro na wannan rana ya maida hankali ne kan yadda tawagar kwallon Najeriya Super Eagles ta kaurace wa buga wasa da takwararta ta Libya sakamakon taskun da suka ci karo da shi lokacin isarsu a lasar ta Libya. Tuni gwamnatin Najeriya ta gayyaci jakadan Libya da ke Abuja don bayyana rashin amincewa da yadda aka tozartar da ƴan wasan na Super Eagles, lamarin da ake ganin cewa ya fara daukar sabon salo daga wasanni zuwa siyasa. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin........
-
Ra'ayoyin masu saurare kan kwace wa mutane 9 shaidar zama ɗan ƙasa a Nijar
14/10/2024 Duração: 09minGwamnantin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta sanar da ƙwace wa mutane 9 dukanninsu makusanta ga hamɓararren shugaban kasar Mohamed Bazoum shaidar zama ɗan ƙasa saboda zarginsu da shirya wa ƙasa zagon-ƙasa. Tsohon madugun ƴan tawaye Rissa Ag Boula da kuma Janar-Janar biyu na soji na daga cikin waɗanda wannan mataki ya shafa. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a
-
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa da dama
11/10/2024 Duração: 10minA kowacce ranar Juma'a, RFI Hausa na bai wa masu saurare damar tofa albarkacin bakinsu dangane da batutuwan da ke ciki musu tuwo a kwarya. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin
-
NNPCL ya sake ƙara farashin man fetur da kashi 15 cikin 100
11/10/2024 Duração: 10minNajeriya ta yi sabon ƙarin farashin mai da akalla kashi 15%, wanda kuma shi ne karo na 4 a cikin watanni 16 da shugaba Bola Tinubu ya shafe kan karagar mulki. Babu dai wani dalili da kamfanin NNPCL da ke matsayin wakilin gwamnati a harkar mai ya bayar dangane da wannan farashi, illa kawai jama’a sun gan shi ne haka kwatsam.Kan wannan batu shirin 'Ra'ayoyin Masu Sauraro' na ranar Alhamis ɗin nan ya bayar da damar tattaunawa akai.
-
Ra'ayoyin Masu Saurare kan ribar da bankunan Najeriya ke samu duk da ƙuncin rayuwa
09/10/2024 Duração: 10minA Najeriya, yayin a ke fama da matsalar tattalin arziki da tsanantar harkokin rayuwa, alkaluma na tabbatar da cewa bankunan ƙasar na ci gaba samun gagarumar riba a kowace rana ta Allah. Shin ko meye dalilin wannan gibi tsakanin bankuna da kuma al’umma? Wane gyara ya kamata ayi domin tabbatar da cewa arzikin kasa na zagayawa a cikin al’umma? Wannan shine maudu'in da masu sauraro suka tattauna akai.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan ingancin dimokuraɗiyya a Najeriya
08/10/2024 Duração: 09minA Najeriya, yanzu haka wasu sun fara nuna fargaba a game da yadda tsarin dimokuradiyya ke gudana a kasar, musamman lura da yadda da zarar aka gudanar da zaben kananan hukumomi, to ko shakka babu jam’iyyar da ke rike da kujerar gwamna ce za ta lashe zaben babu tantama. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka bai wa kananan hukumomin damar cin gashin kansu.Abin tambaya anan shi ne, me ya sa a kullum jam’iyya mai rike da mukamin gwamna ce ke lashe zaben kananan hukomomi a Najeriya?Meye tasirin hakan game da fatan da ake da shi na ganin cewa al’umma ta morewa tsarin dimokuradiyya daga tushe?Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a
-
Ra'ayoyin masu saurare kan rikicin Gaza da ke cika shekara guda
07/10/2024 Duração: 09minYau 7 ga watan oktoban shekarar daya kenan da mayakan Hamas suka kaddamar da hare-hare a Isra’ila, inda suka kashe mutane 1 da 200 tare da yin garkuwa da wasu akalla 150. Wannan ya fusata Isra’ila inda ta mayar da martani ta hanyar kashe sama da mutane kusan dubu 43 a yankin Gaza, tare da yaduwar wannan rikici zuwa kasashen Lebanan da Iran.Shin me za ku ce a game da wannan lamari da ke kara jefa cikin zaman zullumi?Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin